By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayar da umarnin raba dubunnan bahuna da katon iri-iri na kayan abinci ga gidaje sama da 120,000 a jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: Alfahari 2023: Zan Doke Tinubu, Amaechi, Okorocha A Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa – Yahaya Bello
Wata sanarwa da babban daraktan hulda da manema labarai, Ismaila Uba Misilli ya fitar a ranar Asabar, ta nuna cewa gwamnan ya amince da raba kayan abinci cikin gaggawa a unguwanni 114 na jihar a wani bangare na tallafin watan Azumin Ramadan ga marasa galihu.
Ya ce za a raba kayayyakin ne ga magidanta da ke unguwanni da kungiyoyin addini da kuma wasu kungiyoyi a fadin kananan hukumomi 11 na jihar.
Ya bayyana cewa kayayyakin da za a raba sun hada da buhunan suga guda 25,000, buhunan shinkafa 15,000, gallon din man girki 15,000, da kuma kwali 15,000 kowannensu na Taliya da tumatirin sarrafa abincin bi da bi.
Ya ce tallafin da gwamnan ya yi na bayar da agaji ne musamman ga marasa galihu a cikin al’umma a cikin watan Ramadan.
“Don ganin an gudanar da aikin raba kayayyakin a fadin kananan hukumomi 11, Gwamna Yahaya ya amince da tsarin da shugabannin kananan hukumomin za su aiwatar a yankunansu tare da ‘yan majalisar dokokin jiha a matsayin mambobin kwamitin.
“Sauran mambobin kwamitin sune kwamishinoni da shugabannin jam’iyyun siyasa, yayin da manyan mataimaka na musamman kan hulda da jama’a za su kasance a matsayin sakatarori,” in ji Misilli.
Comments 1