Ramadan: Jihar Jigawa ta rage lokacin aiki ga Ma’aikata da wasu awanni
Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da rage lokutan aiki da awanni biyu a cikin azumin watan Ramadan na shekarar 2023.
Shugaban ma’aikatan, Alhaji Hussaini Ali Kila ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN:NCoS Ta Lalata Kayayyakin Da Aka Kwace Daga Fursunonin Da Suka Kai Sama Da N150m
Sanarwar ta ce, yanzu haka ma’aikatan jihar za su kai rahoto ofishin da karfe 9 na safe kuma za su rufe da karfe 3 na rana tsakanin Litinin zuwa Alhamis, maimakon karfe 5 na yamma.
“Yayin da ranar Juma’a, ma’aikata za su bayar da rahoto da karfe 9 na safe kuma za su rufe da karfe 1 na rana,” in ji shi.
Ya ce an yi hakan ne don baiwa ma’aikatan gwamnati damar yin shiri don hutun watan Ramadan da kuma samun karin lokacin gudanar da ayyukan ibada na watan Ramadan.
A wani labarin kuma:Zamba Ta Intanet: EFCC Ta Kama Wani Malamin Addini Da Wasu Mutane 27
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, a ranar Alhamis, ta kama wasu mutane 28 da suka hada da wani malamin addini da ake zargin yan “Yahoo-Yahoo boys” ne a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin ne suka kama shi a Unguwar Mandate, da ke Ilorin, ya biyo bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ‘yan damfarar da ke aiki a yankin.