Ramadan: Ma’aikatar Shari’a a Katsina ta horas da Malamai akan Tafsiri
Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Katsina ta ce ta horar da malaman addinin Islama kan tafsirin Alkur’ani (Tafsir) domin inganta koyarwar Alkur’ani a lokacin azumin Ramadan da ke tafe da kuma bayansa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa malaman addinin Musulunci na gudanar da tafsirin Alkur’ani (Tafsiri), musamman a lokacin azumin watan Ramadan domin ilmantar da Musulmi a kan koyarwar Musulunci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dangote Ya Doke Hamshakan Masu Kudin Duniya 4 Tare Da Shigewa Gaban Su
Shugaban hukumar Dr Muhammad Abubakar ya ce sun gudanar da horaswar ne domin nuna wa malaman muhimmancin inganta hadin kai da zaman lafiya tare da yin addu’o’i a cikin koyarwarsu.
Ya kuma jaddada bukatar malamai su fahimci kansu, su sani cewa aikinsu shi ne isar da sakon Allah Madaukakin Sarki ga al’ummarsu.
Abubakar, wanda shi ne Grand Khadi na jihar, ya ce mutane sun yi ta addu’ar Allah ya ba shugabanni nagari a lokacin babban zabe.
“Mun yi imani cewa Allah ya karbi addu’a. Muna bukatar zaman lafiya fiye da kowane lokaci domin babu abin da za a samu in ba zaman lafiya ba,” inji shi.
Hakazalika, babban alkalin jihar, Mai shari’a Musa Danladi-Abubakar, ya bukaci malamai da su yi amfani da hikima wajen amsa tambayoyi a yayin gabatar da Tafsiri, inda ya kara da cewa malaman su ma shugabanni ne kuma za a tambaye su a ranar kiyama kan rawar da suka taka.
Hakazalika, tsohon Grand Khadi na jihar, Alhaji Ahmad Batagarawa, ya jaddada cewa dole ne malaman da za su gudanar da Tafsiri su kasance da ilimin addinin Musulunci, su kasance masu kyawawan halaye da aiki da koyarwar addinin Musulunci.
A nasa bangaren, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Isa Dodo, ya bukaci malamai da su rika yi wa mutane wa’azi don tabbatar da tarbiyyar ‘ya’yansu.
Ya bukaci gwamnatoci da su kara kaimi wajen horar da daliban makarantar Alkur’ani sana’o’in hannu, domin su zama masu dogaro da kai da hana barace-barace a kan tituna.
A wani labarin kuma:Dangote Ya Doke Hamshakan Masu Kudin Duniya 4 Tare Da Shigewa Gaban Su
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya yi watsi da wani shafin Twitter na bogi da aka rubuta da sunan sa.
Wani mai riƙe da shafin da har yanzu ba a san kowa ne ne ba ya yi amfani da sunansa wajen furta munanan kalamai ga gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Adamawa, Sanata Aishatu Dahiru (Binani).