Dan wasan kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya samu karin magoya baya aa yanar gizo bayan sakon da ya aike wa musulmi na murnar zagayowar watan Ramadan. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ramadan, wata na tara a kalandar Musulunci, lokaci ne na ibada tare da azumi da addu’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutumin da ya sha kwata don murnar nasarar Buhari a 2019 ya fice daga APC ya koma PDP
Ana sa ran Musulmi su kaurace wa ci da sha tsakanin ketowar alfijir har zuwa faduwar rana a wannan lokacin, sai dai su yi buda baki bayan faduwar rana.
Ibadar zai kasance tsakanin 22 ga Maris zuwa 21 ga Afrilu na wannan shekara.
Ronaldo, wanda ya koma Saudiyya da taka leda, ya yi amfani da wannan damar wajen yi musu barka da shigowa watan azumin Ramadan.
A sakon da ya wallafa a shafin Twitter ya ce:
“Ramadan Mubarak ga kowani Musulmi.”
Sakon ya burge magoya bayansa, inda da yawa suka godewa Ronaldo bisa wannan sako daya wallafa.
A wani labarin kuma, An bayyana Kocin da Perez ya fi so ya gaji Ancelotti a Real Madrid:
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez ya bayyana kocin da ya fi so ya gaji Carlo Ancelotti a kungiyar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Real Madrid za ta iya fara neman sabon koci nan da watanni masu zuwa idan Ancelotti ya bar aikinsa a karshen kakar wasa ta bana.