Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Najeriya musamman mazauna kasar Rasha cewa kasar karkashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta samu canji mai kyau da ci gaba, Tribune Online ta rawaito.
Ya ba da wannan tabbacin ne yayin wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna birnin St. Petersburg na kasar Rasha.
KARANTA WANNAN: Kwara: Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Kadarorin da Darajarsu Ta Kai Miliyan N148.7m
Mataimakin shugaban kasar wanda ya gana da su a yammacin ranar Juma’a, ya yi jawabi kan matsalolin da al’ummar suka nuna.
Ya ci gaba da cewa, “Ku tabbata a cikin watanni 9 zuwa 12 masu zuwa, za a samu sauyi cikin sauri a arzikin Nijeriya. Ina magana ne da dukkan ma’ana da kuma alhaki saboda na yi imani da iyawa da jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
A cewar wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola ya fitar ranar Asabar, yace Shettima ya yi magana game da kokarin da gwamnatin ke yi na sake farfado da tattalin arzikin kasar.
Sannan “Ya kuma jaddada aniyar kammala ginin katafariyar masana’antar karafa ta Ajaokuta da kuma farfado da Kamfanin Aluminium Smelter Company of Nigeria (ALSCON).
“Zai zama mai canza wasa. Samun masana’antar ƙarfe mai ƙarfi yana da mahimmanci don ɗaukar nauyin masana’antu na kowace ƙasa, zan iya yi muku alkawarin cewa shugaban kasa zai kawo wa Ajaokuta gaskiya.”
“Ku tabbata cewa idan akwai gado guda daya da Shugaba Tinubu zai yi wa ‘yan Najeriya wasiyya, Ajaokuta daya ce. Zan dawo Rasha, za mu gudanar da wannan tsari, kuma shugabana, maigidana – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sadaukar da kai ga Ajaokuta da ALSCON.
“Mun fara tattaunawa, kuma za mu ga cewa wadannan kamfanoni biyu sun tashi; ba mu da wani zabi da ya wuce mu kawo su ga gaskiya,” in ji mataimakin shugaban kasa Shettima.
Da yake karin haske game da sauye-sauyen da Najeriya za ta samu, mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin Tinubu za ta yi amfani da dimbin albarkatun bil’adama da na abin duniya don dora kasar nan kan turbar ci gaba mai dorewa.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana kwarin gwiwa ga karfin Shugaba Tinubu na kawo sauyi a Najeriya, yana mai cewa “Shugaban kasa ya yi imani da aikin Najeriya sosai,” kuma bayyanarsa a matsayin shugaban kasa “ba ta samu kwatsam ba.”
Da yake ba da misalan fitattun ayyukan da shugaba Tinubu ya yi a matsayin gwamnan jihar Legas, Sanata Shettima, ya ce shugaban ya nuna “Hanzarin zaburar da ci gaba a kowane fanni, kuma ya nuna kishi da kuma himma wajen kawo sauyi a Nijeriya.”
“Wakilan al’ummar Najeriya a jawabansu daban-daban, sun yabawa shirin gwamnatin Tinubu na yin cudanya da gwamnatin kasar Rasha domin kyautata alaka tsakanin Najeriya da Rasha.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Ambasada Shehu Abdullahi; Babban Sakatare, Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Mista Gabriel Aduda; babbar Sakatariyar, Ma’aikatar Ma’adanai da Raya Karafa, Misis Mary Ogbe; Shugaban kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar Rasha, Dr Maurice Okoli, da shugaban ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDO), Mista Sampson Uwem, da dai sauransu.
A wani labarin kuma, Gwamnan PDP Ya Biya Kashi Na Uku Na Rabin Albashin Ma’aikata
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya amince da biyan wani bashin rabin albashi tare da albashin ma’aikatan jihar na watan Yuli.
Mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Osogbo a ranar Asabar din nan.