Gwamnan Amhara dake yankin Arewa maso yammacin kasar Habasha ya bukaci Rasha da ta tallafawa gwamnatinsa domin sake ginawa al’umar yankin ababen mure rayuwa da aka lallata yayin rikicin baya-bayan nan a yankin.
Kafar yada labarai ta yankin na Amhara ta ruwaito ce Yilkal Kefale ya gana da Jakadan Rasha a Habasha Evgeny Terekhin a ranar Litinin inda suka tattauna batutuwa kan yunkurin sake gina birnin.
A cewar Gwamnan yankin Rasha ta amince tayi aiki tare da cibiyoyin Ilimi na Amhara domin bunkasa fannin.
Kazalika Gwamnatin yankin ta ce, Yan tawayen TPLF sun lalata ababen mure rayuwa lokacin da suka kwace Iko da birnin a shekarar da ta gabata.