Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu Peter Obi ya bayyana bakin cikinsa kan ficewar babban kamfanin harhada magunguna, GlaxoSmithKline (GSK), daga Najeriya bayan shafe shekaru 51 yana aiki
Obi, a cikin jerin sakonnin twitter, ranar Asabar, ya ce dalilin da kamfanin ya bayar na barin yana nuna makoma mai cike da bakin ciki ga yanayin saka hannun jari na kasar
Ya ce A yau, na yi bakin ciki da na ji cewa GlaxoSmithKline (GSK), na ficewa daga Najeriya bayan shafe shekaru 51 yana aiki
Dalilin da suka sa na ficewa daga Najeriya ya fi bacin rai, kasancewar sun daina ganin ci gaban kasar nan gaba, wanda za a dora shi kan samar da albarkatun mai
Shi ma tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce muna kan tafiyar al’ummarmu inda ’yan kasa da kasa ke barin kasar kuma na gida ke rufe shagunansu
KARANTA NANJirgin Nigerian Air Zai Fara Aiki A Watan Oktoba
Wannan, in ji shi, duk sakamakon rashin tafiyar da tattalin arzikinmu ne kamar yada ya dace sakamakon haka, miliyoyin mutane suna rasa ayyukansu, kuma alkaluman talaucin da muke fama da shi na kara ta’azzara, duk da cewa mun riga mun zama helkwatar talauci a duniya
Obi ya kuma ce Wadannan ’yan kasa da kasa da ke barin kasarmu, ba wai kawai samar da ayyukan yi ba ne, amma suna samar da horo maras kima wanda ke ba da gudummawa ga ci gaban jarin dan Adam
GSK wacce ke da masana’anta da aka kafa a Agbara, a sama da hekta 25 na fili a Agbara, ta dauki ma’aikata sama da 400 kwararru kai tsaye kamar masana harhada magunguna, masana kimiyyar kere-kere, likitocin biochemists, chemists, likitocin hakori, likitoci da sauransu
Sannan kuma sun dauki wasu ma’aikata sama da 1000. . A fakaice ta samar da ayyukan yi da kasuwanci ga dubban ‘yan Nijeriya a fadin kasar nan. Yanzu suna barin duk waɗannan a baya, kuma suna tura ƙarin mutane zuwa cikin rashin aikin yi
Jaridar Vanguard ta ruwaito dan takarar na LP ya tuno da daidaiton matsayinsa cewa “domin juyar da al’ummarmu, dole ne mu matsar da tattalin arzikin daga amfani zuwa samarwa, wanda wani bangare nasa ya hada da karfafawa da tallafawa zuba jari na gida da waje, kamar GSK, a cikin kasar
A WANI LABARIN KUMANa Rasa Jikana Saboda Rashin Kulawar Likitoci A Asibitin Gwamnati-Akpabio
Obi ya kuma jaddada mahimmancin samar da yanayi da zai samar da kuma dorewar ‘yan kasa da kasa don saka hannun jari a kasarmu
Inda ya ce shi ne mabudin burinmu na daukaka. A cikin sabuwar Najeriya da muke neman kirkirowa, fifikon samar da kayayyaki zai karfafa masu zuba jari su tsaya su fadada a kasarmu