Rashin aiwatar da Manufofi yadda ya dace , ke da alhakin Wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke sha – Sanata Moro
Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, kuma Sanata mai wakiltar mazabar Benuwe ta Kudu Abba Moro ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala a halin yanzu saboda rashin aiwatar da manufofin Gwamnati da aka bijiro domin inganta rayuwarsu.
Moro wanda ya bayyana hakan a Makurdi ta Jihar Binuwai yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a karshen mako, ya yi tir da yadda matsalolin da ke addabar kasar nan, ya nuna cewa Majalisar dattawa za ta yi duk mai yiwuwa don dakatar da wannan lamarin.
Yayin da Majalisar Dattawa ta dawo da zaman ta, ina tabbatar muku da cewa za mu bi diddigin al’amuran da suka shafi al’ummarmu, saboda mu ne muka fi kusa da su kuma muna jin radadin abinda ke damun su.
KARANTA NAN:Ƴan Najeriya sun fi talauci a karkashin gwamnatin Tinubu – Ndubuisi Ekekwe
‘Yan Najeriya na shan wahala a yau saboda rashin aiwatar da tsare-tsare da ke da nufin inganta rayuwarsu, Za mu dora kanmu wajen yin tunani, mu fito da tsare-tsaren da za su yi mana amfani baki daya,” inji shi.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Jihar Katsina ta ɓullo da Hanyar Bunƙasa Ilimi tun daga matakin Farko
Gwamnatin Jihar Katsina ta ɓullo da Hanyar Bunƙasa Ilimi tun daga matakin Farko
Gwamnatin Jihar Katsina ta ɓullo da wasu sabbin tsare-tsaren da zasu kara inganta harkokin Ilimi tun daga tushe a Jihar.
Shugaban Hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar SUBEB, Dr. Kabir Magaji ya bayyana hakan, a yayin wani zaman na musamman da ya gudana a ɗakin taro dake Hedkwatar Hukumar dake Katsina.
Kamar yadda ya bayyana wasu daga cikin waɗan nan sabbin Matakai sun haɗa da;
Sakamakon wadatatun Malamai da Gwamnatin Jiha ta ɗauka a Makarantun mu, za mu rage Cinkoson Ɗalibai, ta hanyar maido da tsarin Karatun Safe da yamma, a wasu daga cikin Makarantun dake fama da matsin cinkoson Ɗalibai a Azuzuwa.
Haka kuma, daga yanzu laifi ne Maigirma ga duk Malamai da aka samu da ɗaukar Sojan Gona, domin riƙa shigar masa Aji yana biyan sa, don haka duk wanda aka samu da hannu cikin a wannan laifi zai fuskanci hakuncin da ya dace da shi.
Kazalika, duk Malamin da Makarantar sa ta tura ya zuwa wani shirin horaswa, ya zama wajibi ya dawo Makarantar sa ya horos da sauran Malamai ƴan uwan sa, akan ilimin da ya samu.
Sakamakon wannan mataki, an Umarci duk kanin Sakatarorin ilimi, da