Rashin kyakkyawan Shugabanci ne ya haifar da rashin tsaro a Najeriya – Peace Corp’s Commandant
Kwamandan Hukumar tabbatar da zaman lafiya ta kasa Peace Corps of Nigeria (PCN) Dickson Ameh Akoh ya ce rashin Shugabanci da rashin kula da albarkatun kasa ne ke haddasa rashin tsaro da ke addabar lungu da sako na kasar nan.
Sai dai ya roƙi Ƴan Ta’addan da kungiyoyinsu da ke addabar al’umma a kasar nan da su yi watsi da makamansu, su rungumi zaman lafiya don dawo da al’umma kan turbar ci gaba mai ma’ana.
Ambasada Akoh ya kuma buƙaci matasa da su haɗa kai da Hukumomi a kasar nan domin kawo karshen ’yan fashi da makami da sace-sacen Jama’a da sauran munanan dabi’u da ke kawo cikas ga ci gaban kasar nan.
Shugaban Hukumar tabbatar da zaman lafiya, ya yi jawabi a Abuja a yayin bikin ranar zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya na bana mai taken “Ayyukan samar da zaman lafiya; Burinmu Ga Manufofin Duniya”.
KARANTA NAN:Gwamantin Tarayya ta sha alwashin Tallafawa Manoman Citta da cutar Fungal ta illata Gonakinsu
Akoh ya ƙalubalanci ‘yan Najeriya da su yi amfani da ranar zaman lafiya ta duniya ta bana domin zurfafa tunani kan ƙalubalenn da ƙasa ke fuskanta tare da haɗa kai wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’umma masu zuwa.
Ya ce muhimmancin wannan rana ya kamata a tunatar da kowa da kowa, ya kamata a yi ƙoƙarin kare hakkin dan Adam da nufin samar da zaman lafiya da haɗin kai ba tare da nuna kabilanci ko bambancin addini ba.
Ya kuma ce, “Muna fuskantar babbar barazana guda ɗaya a ƙasar nan, wanda shine rashin tsaro. Abubuwan da ke haifar da rashin tsaro a Najeriya a yau suna faruwa ne saboda shugabanci mara kyau da kabilanci, da masu tsattsauran ra’ayin addini, rashin aikin yi da take haƙƙin Ɗan Adam da kuma makauniyar biyayya ga ‘yan siyasa masu son kai.
“Ba tare da la’akari da bambancin kabilancinmu na siyasa da addini da zamantakewa ba, ya zama wajibi a gare mu mu haɗa kai, mu ƙulla alaƙa mai ƙarfi a cikin gida da waje da nufin samar da tsaro da zaman lafiya mai dorewa”, inji shi.
Haka kuma yace “Bai kamata mu sanya son zuciya a fannin zaman lafiya ba, maimakon haka mu ba shi fifiko, haka nan kuma mu mayar da hankalinmu wajen ci gaba da addu’o’i ga wadanda ke kan gaba wajen yakar duk wani nau’in rashin tsaro tare da yin addu’ar Allah ya jikan sojojinmu da suka mutu a filin daga,
a takaice a sahun gaba na yakin kare martabar yankin Najeriya”
Shima da yake Jawabi a wajen taron babban sakataren Ma’aikatar Matasa ta Tarayya Ismaila Abubakar ya ce babu wani ci gaba mai ma’ana da za a samu idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A cewarsa barnar ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane shaida ce ƙarara akan halin rashin tsaro da kasar ke ciki, kuma suna hannu wajen haifar da rashin zaman lafiya da ɗar-ɗar a cikin zukatan ƴan Najeriya.
Babban Sakataren ya kalubalanci ’yan Najeriya da su yi amfani da majami’u da masallatai wajen yada sakonnin zaman lafiya, da zama jakadun zaman lafiya ta yadda za a samu kasar Nijeriya da ba ta da tashin hankali.