An bayyana rashin kyawun hanyoyin zirga zirga na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin tsaro dake ci gaba da addabar wasu yankunan Arewa maso Gabas.
Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da abubuwa 11 da ta fitar a karshen taronta na 9 da ta gudanar a Yola, Jihar Adamawa a ranar Asabar.
Karanta nanMataimakin Gwamna Obaseki Ya Bayyana Ranar da Zai Ayyana Aniyarsa taTsayawa Takarar Gwamna
Sanarwar da Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya sanya wa hannu, wanda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karanta, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda yankin ke fama da talauci.
Sun kuma nuna damuwarsu akan cewa an yi watsi da hanyoyin Tarayya a ciki da tsakanin jihohin yankin. Don haka ta yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta bi diddigin kwangilar hanyoyin da aka bayar a yankin,” in ji su.
Wani batu da ya dame shi da dandalin ya gabatar shi ne na rashin kyawun tsarin layin dogo a yankin da zai hada duka jahohin domin saukaka kasuwanci.
Hakazalika ya lura cewa gyare-gyaren da aka yi akan tsoffin layin dogo ba su da amfani da fasaha mai dorewa.
A wani labarin kumaMataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gana da Wasu Gwmnoni a Ogun, Ya Bukaci Hadin Kan Najeriya
Majalisar ta yi kira da a shigar da yankin cikin tsarin sufurin jiragen kasa na Najeriya ta hanyar amfani da layin dogo na zamani da kuma tsarin titin kasa wanda yankin ya bace a fili”, in ji ta.
A cewar sanarwar, kungiyar ta yanke shawarar gudanar da taro karo na 10 a Bauchi tsakanin 23 ga Fabrairu zuwa 26 ga Maris, 2024.