Gwamnatin jihar Borno ta ce akwai yara miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin damuwa.
Kwamishinan ilimi mai zurfi, Abba Wakibe ne ya bayyana haka a yayin bikin bude horas da shirin ‘A Risk Children-Programme (ARC-P)’ na malamai 968’ a jihar Borno da aka gudanar jiya a Maiduguri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Jihar Eikiti Oyebanji Ya Nada Masu Ba Da Shawara Na Musamman Guda Takwas
Ya kuma jaddada cewa tashe-tashen hankula sun yi tasiri sosai a fannin ilimi, ciki har da shigar yara da ma’aikata.
“Muna da marayu 56,000 da zawarawa 49,000, amma har yanzu ba a san adadin ’ya’yan marayun ba. Fatanmu ne cewa wannan shirin zai rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Borno,” inji Wakibe.
Ko’odineta na (ARC-P), Hajiya Inna Galadima, ta ce an zabo malamai 968 a fadin kananan hukumomin jihar 27 na tsawon makonni uku domin ba su horon da ake bukata.
Ta ce shirin zai yi matukar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
A WANI LABARIN KUMA: Ka Gaggauta Cire Tallafin Man Fetur – Shawarar Elrufa’i Ga Buhari
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta cire tallafin man fetur.
El-Rufai ya yi wannan kiran ne a taron jihohi na NESG, wanda ya gudana jiya a Abuja.
Da aka tambaye shi yayin zaman cewa me ya kamata gwamnati ta sa gaba, gwamnan ya ce, “a cire tallafin man fetur nan take.
Comments 2