Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ayyana dokar ta baci a kananan hukumomi uku na jihar, bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da; Anka, Bukkuyum da kuma karamara hukumar Gummi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaron Kasa
Gwamna Matawalle ya kuma bayar da umarnin dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar nan take ciki har da taron jam’iyyar APC har sai an sanar da shi, a wani mataki na saukaka kokarin jami’an tsaro na fatattakar masu aikata laifuka a yankunan.
Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce an dakatar da taron ne domin dakile yawaitar hare-hare a garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.
Ya ba da umarnin rufe kasuwannin Danjibga da Bagega da Colony zuwa titin Lambar Boko, Bakura zuwa titin Lambar Damri, Mayanchi- Daki Takwas zuwa titin Gummi, Daki Takwas zuwa titin Zuru, Kucheri- Bawaganga – titin Wanke, Magami zuwa Dangulbi, sai Titin Gusau zuwa titin Magami.
Gwamnan yayin da yake nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ‘yan bindiga suka sake kunno kai da kuma kashe-kashen da aka yi wa wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a baya-bayan nan a kananan hukumomin Gusau, Tsafe, Gummi, Bukkuyum, Anka Bungudu, Maru, Maradun da Kaura Namoda, ya kuma shawarci duk masu ruwa da tsaki da aka gayyata zuwa taron jam’iyyar APC na ranar Juma’a da za a yi su jira wata sabuwar rana.
Sai dai gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tunkari wadanda aka samu da saba wannan umarni.
A wani labarin kuma, Mutane 440 Din Da Buhari Ya Karrama Kamata Yayi Su Kasance A Gidan Yari – Galadima
Tsohon aminin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya caccaki karamcin kasa da shugaban kasar ya baiwa wasu mutane kwanan nan.
Ya yi zargin cewa daga cikin wadanda aka yiwa karramawa 470, kasa da 440 daga cikinsu ya kamata su kasance a gidajen yari a fadin kasar nan.