Rashin tsaro a Ughelli da kewayenta a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta, na ci gaba da tabarbarewa sakamakon wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka kashe ‘yan sanda guda uku.
Lamarin ya faru ne a wani wurin mai abinci a daren Lahadi. Sai dai wannan harin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani sabon Jami’in ‘Yan sanda na Shiyya, DPO, Mista Benjamin Igometi ya karbi ragamar jagorancin Ughelli.
Ko da yake jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, Onome Onowakpoyeya har yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba a sanda aka tuntube shi, wata majiya a inda lamarin ya faru ta ce maharan sun tafi da ‘yan sanda da aka kashe ba tare da saninsu ba, suka harbe su a kusa da kusa suka gudu da bindigoginsu.