Rashin tsaro: Zamu yaƙi ƴan ta’adda a Abuja – Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin kai yaki ga masu aikata laifukan da ke addabar Abuja.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da ginin titin Paikon-Kore a yankin Gwagwalada ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:Cire tallafin mai: ‘Za mu rage farashin sufuri da kashi 50%’ – FG
Ministan ya sha alwashin mayar da babban birnin tarayya Abuja wurin zaman lafiya.
“Na tabbatar muku a baya cewa za mu dauki wannan yaki da su gaba daya. Yau ka ga ba mu kyale su ba. Na ce muku duk wadannan masu laifi za su gudu.
“Za mu tabbatar ba su sake yin barci ba. Idan suka ce ba za mu yi barci ba, su ma ba za su yi barci ba. Yaron da ya ce uwar ba za ta yi barci ba, zai yi barci? Don haka, muna kai musu yakin gaba-gaba. Su jira mu; za su ga wuta ga wuta,” inji shi
A wani labarin kuma:Zaben Cike Gurbi: INEC ta fara rabon kayan zaɓe a Bauchi
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta fara raba wasu muhimman kayyayaki gabanin zaben da za a sake gudanarwa a jihar Bauchi a ranar 3 ga watan Fabrairu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Kotun daukaka kara ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a mazabu 42 da ke mazabun majalisun jihohi hudu da suka hada da Bauchi ta tsakiya, Zungur-Galambi, Ningi 1, da Madara-Chinade.