Ribadu Ya Yi Ganawar Sirri Da Gwamnonin Kudu Maso Gabas
Mai bada shawara kan harkokin tsaro na Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Nuhu Ribadu, ya gana da gwamnonin jihohin Kudu-maso-gabas guda biyar a Abuja a ranar Litinin.
Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron na sirri ba, akwai hasashe na cewa ba zai rasa nasaba da tabarbarewar tsaro a jihohin Anambra, Enugu, Abia, Imo, da Ebonyi ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Budurwa Ta Yiwa Saurayinta Tofin Alatsine A Shafin Facebook
A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar Dattawa ta yi Allah-wadai da zaman gida na ranar Litinin a shiyyar siyasar yankin Kudu maso Gabas tare da neman Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da Gwamnatin kasar Finland tare da mika mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, domin gurfanar da shi gaban kuliya.
Babban zauren majalisar ya yanke shawarar gayyatar Ministan Harkokin Waje (lokacin da aka nada) da masu ruwa da tsaki don gudanar da cikakken bincike tare da kawo wasu masu daukar nauyin wannan doka.
Majalisar dattawan ta kuma yi watsi da shawarar a saki shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, inda ta ce hakan zai kai ga yanke hukunci saboda sakin sa na nan a kotu.
An ce wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ne ke aiwatar da dokar zaman gida ba bisa ka’ida ba a jihohi biyar na Kudu maso Gabas.
A shekarar 2021 ne aka ayyana dokar da ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar, domin matsawa gida bukatar a saki shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, wanda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tsare tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin ta’addanci.
A wani labarin kuma:Majalisar Dattawa ta shirya shiga tsakanin FG, NLC don dakatar da yajin aiki
Majalisar dattijai ta umarci shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da daukacin shugabannin majalisar dattijai da su shiga tsakani tsakanin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da gwamnatin tarayya domin dakile yajin aiki.
Hakan ya zo ne a yayin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce kudaden da suke samu a majalisar dokokin kasar bai isa su kula da kansu ba.