Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya abu ne da ya zama ruwan dare a Kasashen Afrika, wanda Najeriya ta na daya daga cikin kasashen da wannan lamarin ya ke addaba, kusan ko wace shekara.
Hakan ya sa Gwamnatoci, Sarakunan Gargajiya, Kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki, su ke neman hanyoyin kawo karshen wannan matsala.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bazan auri Jahilin Miji ba cewar Maimunat Muhammad
A Najeriya, Jihar Yobe ita ce ta uku a yawan dabbobi, don hakane Gomnatin Jihar ta ke bin dukkan hanyar da ta dace, wajen ganin ba’a samu matsala ba.
Daga cikin hanyoyin kuwa, akwai yunkurin tabbatar da Sulhu a tsakanin bangarorin biyu a ko da yaushe, wanda hakan ya haifar da kafa Kwamitin Sulhu da ake kira da “Zauren Sulhu”.
A bangare guda kuwa, Gwmnatin Jihar tare da hadin gwuiwar Kungiyoyin agaji na duniya, ta na cigaba da fadakar da manoma da makiyaya yadda za’a zauna lafiya da juna.
Wannan yana ci gaba da wanzuwa inda a ranar 11 ga watan Agusta 2021, Kungiyar tarayyar Turai EU da majalissar zartarwar kasar Burtaniya, tare da hadin gwuiwar Gwamnatin Jihar Yobe, su ka shirya taron fahimtar juna, akan tsarin da ya dace a bi don kauce wa rikicin manoma da makiyaya a Jihar Yobe.
A Jawabin ta jim kadan bayan soma taron, Komishiniyar Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa, Dr. Mairo Ahmed Amshi ta ce Gwamnatin Jihar Yobe ta na iya kokarin ta, domin hana aukuwar rashin jitu wa tsakanin manoma da makiyaya, inda yanzu haka ma ta samu amincewar Gwamnatin Tarayya na gina cibiyar bunkasa kiwon dabbobi a dajin Jakusko zuwa na Nasari, mai fadin kimanin hekta 49,600 da sauran dazukan kiwon dabbobi.
“Dakile Rikicin Manoma da Makiyaya abu ne da ya ke bukatan hadin kai daga dukkan bangarori, don haka yana da kyau Sarakunan Gargajiya, Gwamnati da Kungiyoyi masu zaman kansu, su tashi tsaye” inji Dr. Mairo Ahmed Amshi.
Tunda farko da ya ke Jawabin maraban baki, Jami’in Cibiyar Sasanta tashe-tashen hankula a Arewa Maso Gabashin Nigeria reshen Jihar Yobe MCN, Mal. Abdul-Kadir Sambo ya ce, manufan taron shi ne, a tattauna yadda za’a kauce wa rashin jitu wa tsakanin manoma da makiyaya.
“A wannan taro, muna bukatar samun shawarwari daga bakin manoma da makiyaya yadda za’a dakile rikici tsakanin bangarorin biyu”, Sambo ya ja hankulan mahalarta taron.
A na su bangaren, wakilan Makiyaya sun ce, dole ne a dauke Gonaki a kan burtalin dabbobi, mashaya da dazukan kiwon su, ya yin da kuwa, manoma su ka ce, ya na da kyau ayi hakan, amma a dubi yadda al’uma ta ke kara yawaita, wanda hakan ya ke haifar da bukatar samun gonaki da yawa.
Taron dai ya samu halartar Komishinan Ma’aikatar Shari’a Barister. Saleh Samanja, da Shugaban Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi Dr. Idriss Yusuf Madaki, da Wakilan Komishinan, Yan Sanda da Hukumar Tsaron Farar Hula da kula da kaddarorin Gwamnatin wato Civil Defense, da Sarkin Damaturu, Kunyoyin Manoma da Makiyaya da sauran su.
Comments 1