Rikicin Ribas: Ba Zamu Taɓa Komawa PDP Ba – Dan majalisa
Enemi George, daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da suka koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya ce ba zai koma jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, tsohuwar jam’iyyarsa ba.
George ya bayyana cewa 27 daga cikin su da suka koma APC sun jajirce wajen goyon bayan shirin ‘Renewed Hope Agenda’ na Shugaba Bola Tinubu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kotun Koli Ta Yi Wani Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan Kano
Ya yi magana ne a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyi a matsayin bako a shirin Siyasar mu a Yau na gidan talabijin na Channels .
“Mun ketare Rubicon. Mun koma APC. Mun zabi shugaban kasa, idan muka ga shugaban ya cancanci kuri’unmu to ina ganin ya dace mu goyi bayansa.
“Mun koma don shiga ajandar sa ta Renewed Hope don yin aiki tare don tabbatar da cewa abin da ‘yan Najeriya ke bukata ya cika,” in ji George.
DAILY POST ta tuna cewa Ribas ta tsunduma cikin rikicin siyasa sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.
Lamarin dai ya janyo rarrabuwar kawuna a majalisar, inda 27 daga cikinsu suka fice daga PDP zuwa APC mai mulki.
A wani labarin kuma:Kotun Koli Ta Yi Wani Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan Kano
Kotun koli ta tabbatar da hukunci a karar da aka shigar kan zaben gwamnan jihar Kano.
A ranar Alhamis ne kwamitin alkalai mai mutane biyar karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ya kebe hukuncin bayan sauraron lauyoyin da ke kan lamarin.