Rikicin Ribas: Ka fice daga PDP, ka dawo Jam’iyyar mu – APC ta zaburar da Wike
Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas, ta yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike da ya koma jam’iyyar saboda yana bukatarsa.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Tony Okocha, ya ce jam’iyyar ce ke kan mulki, don haka ya kamata Wike ya shiga.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dalilin da ya sa muka amince da karin biliyan 4 a kasafin kudi – Majalisar Zamfara
Ya zanta da manema labarai a Fatakwal bayan ‘yan majalisar jihar 27 sun koma APC.
Da aka tambaye shi ko sauya shekar wani bangare ne na shirin Wike ya koma APC, Okocha ya ce: “Bana tunanin haka.
“Ko menene dalilinsu idan sun isa gadar za su tsallaka ta.
‘’Wike dan siyasa ne da sunansa ya girgiza a cikin al’umma; don haka babu wanda zai iya tunani ko ya ce masa idan zai koma APC ko a’a.
“A 2023, ya taimaka kwarai da gaske wajen nasarar APC a jihar.
‘’Abin da ya fi dacewa mu ce ya yi shi ne ya zo ya koma APC domin ita ce ke mulki.
A wani labarin kuma:Gwamnan Sokoto: PDP na neman kotu da ta soke zaben Aliyu
Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna a zaben gwamnan jihar Sokoto da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Saidu Umar, sun lissafo wasu dalilai guda tara da suke neman kotun koli da ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe da kuma na kotun ɗaukaka ƙara wanda ya tabbatar da zaben Ahmed Aliyu a matsayin Gwamna.
A karar da tawagar lauyoyinsu karkashin jagorancin Sunday Ibrahim Ameh, SAN suka shigar a madadinsu, wadanda suka shigar da kara sun yi ikirarin cewa “hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya saba”, don haka ya kamata kotun koli ta kore shi.