Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa masu hamayya da juna a hanyar Zaria dake jihar Kano, akalla mutane 63 da ake zargi jami’an tsaron farin kaya na Najeriya NSCDC ne suka kama.
Magoya bayan jam’iyyar da ke hamayya da juna sun yi amfani da muggan makamai a yayin arangamar da suka hada da kona motoci uku tare da farfasa wata guda inda aka tabbatar da jikkata wasu da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Shugabar Karamar Hukuma Ta Rasu Bayan Halartar Wani Taro Kan Zaben Shugaban Kasa
Da yake yiwa manema labarai jawabi, a jiya, jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC a jihar Kano, Ibn Abdullahi ya tabbatar da kamun, yana mai cewa: “Mun kama mutane kusan 63 da ake zargin ’yan daba ne da ke kawo wa jama’a rashin zaman lafiya, rike da muggan makamai, kona motoci da kwace wa mutane wayoyin hannu.
“Za a bincike su kuma a kai su kotu don gurfanar da su,” in ji shi.
Idan Zaku iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa biyo bayan tsare-tsare na jam’iyyar APC; Jam’iyyar NNPP, da PDP, domin gudanar da taron gangamin yakin neman zabe, rundunar ‘yan sanda a Kano, ta shawarci jam’iyyun siyasa da su dakatar da duk wani gangamin siyasa, domin kaucewa tarzoma, bayan yunkurin cimma matsaya a tsakaninsu ya ci tura.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: An Kama Wani Dan Majalisa Dauke Da Makudan Kudin Kasashen Waje
An kama wani dan majalisar wakilai, Dokta Chinyere Igwe da wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba, Punch ta rawaito.
Igwe, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Fatakwal 2, a majalisar wakilai ta kasa, an kama shi ne da safiyar ranar Juma’a a kan titin Aba a Fatakwal.