Ronaldo Ya Nuna Takaicinsa Kan Wata Alfarma Da Ya Nema Wajan Guardiola
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ki amincewa da damar jagorantar tawagar kasar Brazil, in ji jaridar UK Mirror.
An yi wa Koci mai shekaru 51 ta yin mukamin bayan Tite kafin ya yi murabus daga jagorancin Brazil bayan gasar cin kofin duniya ta 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ku Ƙauracewa duk wani nau’in magudin zabe – Limami ga Ƴan siyasa
Guardiola bai taba yin aiki a matakin kasa da kasa ba amma ya kafa tarihi a matsayin daya daga cikin manyan Masu Horaswa a fagem kwallon kafa, musamman a kungiyon Barcelona, Bayern Munich, da Manchester City.
Tsohon Shahararren dan wasan gaban na Brazil, Ronaldo De Lima, ya tuntubi wakilin Guardiola Pere don ganin ko Tsohon dan wasan na Sipaniya zai yi sha’awar maye gurbin Tite.
Duk da haka, Rahotanni sun nuna cewa, Pep yi watsi da bukatar Ronaldo, inda ya nuna sha’awar ci gaba da zama a Etihad akalla na tsawon shekaru biyu masu zuwa anan gaba, bayan da ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da City a watan Nuwamba wanda ya sa zai cigaba da zama da zakarun Premier har zuwa 2024.
A wani labarin kuma: Allah kaɗai ne zai Iya Hana Tinubu zama Shugaban Ƙasa – Inji Gwamna Arewa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce Allah ne kadai zai iya hana Asiwaju Bola Tinubu ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake jawabi a karamar hukumar Kokona yayin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar a Nasarawa ta Yamma, Architect Shehu Tukur, Sule ya ce gwamnonin APC a arewa za su yi amfani da dukiyar su wajen ganin Tinubu ya samu nasara.