Mutumen Anambra, Mr Olisa Igbonwa daga Alor, Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu dake Jahar Anambra, an samu raɗe-raɗin cewa an binne shi matacce, amma ya dawo raye a hedikwatar Ƴan Sanda ta Awka.
Igbonwa, wani hadimin Ministan Ƙwadago Dr. Chris Ngige a ranar Laraba ya ziyarci Rundunar Ƴan Sandan Jahar Anambra, Awka, inda ya bayyana cewar yana nan a raye, kuma Ba’a binne shi da rai ba, kamar yadda aka bada rahoto.
Akwai wani bidiyo dake yawo cewa wani Chief Olisa Igbonwa an binne shi a raye a Alor, Jahar Anambra daga manyan ƙauyen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yajin Aikin ASUU: Wata Kungiyar Dalibai Ta Bukaci Ministan Ilimi Ya Yi Murabus
Igbonwa dai akwai zargin dake cewa an cire mashi rawani daga Ichie Ngene, matakin daya sanya ake ganin baiyi dai-dai ba, wanda yayi sanadiyar binne shi, daga manyan garin.
Amma Igbonwa wanda yake a ofishin Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sanda ya Jahar, yace yana nan a raye, kuma ba za’a karɓi rawanin sa, duk da gargaɗin da aka yi mashi na binne shi a raye.
Acewar sa, ya karɓi sarauta daga Mai Martaba Sarkin Igwe Alor, amma wani Mr Uzoma Igbonwa da wasu, suna Son karɓe mashi rawanin sa a cikin kwanaki 30 ko kuma ya fuskanci mummunan hukunci.
Amma ƴan sanda a cikin wata sanarwa da suka fitar mai sa hannun DSP Ikenga Tochukwu Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sanda, yace wannan bidiyo da abinda ya ƙunsa ba gaskiya bane.