Hukumar Kwastam ta Najeriya NCS ta ce rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar ba shelanta yaki ne tsakanin kasashen biyu ba, kamar yadda ake hasashe.
Mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga al’ummar Illela da ke kan iyaka da Jihar Sakkwato a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Kotu Ta Dakatar Da Wani Gwamna Daga Yunkurin Tsige Mataimakinsa
Adeniyi, wanda ya je kan iyakar Illela domin sanin matakin da ake bi na bin wannan doka, ya fayyace cewa abin da ke faruwa a Najeriya ma yana faruwa a wasu jihohin yammacin Afirka da ke kan iyaka da jamhuriyar ta Nijar, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
“Burina a nan shi ne in maido da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu, kasancewar ba babban kwamandan Tarayyar Najeriya kadai ba, har ma da shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.
“Kamar yadda muka sani, daya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan shugaban shi ne inganta kasuwanci tsakanin mambobin kungiyar ECOWAS.
“Amma duk mun san cewa kasuwanci ba zai iya faruwa a yanayin da babu zaman lafiya ba. Don haka manufar gwamnati ita ce ta tabbatar da cewa mun yi amfani da karfi sosai kan alakar kasuwanci da tsaro,” inji shi.
A wani labarin kuma, NECO Ta Lashi Takobin Dakatar Da Satar Jarabawa
A yayin da ake ci gaba da gudanar da jarabawar manyan makarantun sakandire ta 2023, shugaban hukumar shirya jarabawar ta kasa Farfesa Dantani Wushishi a ranar Juma’a ya sha alwashin cewa hukumar jarabawar ba za ta amince da ayyukan da ke kawo cikas ga ingancin jarabawar ta a fadin kasar nan ba da suka hada da satar jarabawa.
Wushishi ya yi wannan gargadin ne a Jos ranar Juma’a a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ya zagaya wasu makarantu domin sanya ido kan jarabawar SSCE da ke gudana a jihar Filato.