By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaro na shiyyar Kudu maso Yamma da aka fi sani da Amotekun dake jihar Ogun sun kama wadanda suka kashe wani sufeto ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo.
Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, yace rundunar ta kama wani Aminu Azeez da wasu mutane 14 bisa zargin laifin hada baki da kashe Insifeto Adebayo Adele wanda aka kashe a ranar 20 ga watan Satumba shekarar 2021.
Akinremi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya kara da cewa an kama wadanda suka hada baki a jihar Ogun.
Ya ce an yi wa dan sandan taron dangi wanda aka kashe shi har lahira a lokacin da ya jagoranci tawagar bincike don cafke wadanda ake zargi da sayan shanun sata a Ibadan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar 20 ga watan Satumba, tawagar ‘yan sanda da ke aiki da IGP IRT Annex Ibadan, yayin da ake bincike, sun kai wa wani mai sana’ar sayar da naman mai suna Aminu Azeez,da kuma wasu kimanin mutane 14 hari.