Hedikwatar tsaro a ranar Juma’a ta ce faifan bidiyon da ke nuna Alhassan Ado-Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai a jihar Kano, yana harba bindiga kirar AK-47 yayin da jami’an soji ke kewaye da shi a sansanin horar da sojoji da ke dajin Falgore aka nadeshi. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, lya ce an nadi bidiyon ne a lokacin atisayen horas da sojojin Najeriya bataliya ta 3 inda aka gayyaci dan majalisar a matsayin babban bako.
KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan dokar da ta tilasta wa Tinubu nada ministoci cikin kwanaki 60
Sanarwar ta kara da cewa, “Hedikwatar tsaro tana son bayyana cewa, yada bidiyon wani shiri ne na yunkurin bata-gari na bata sunan rundunar sojin Najeriya a gaban mutanen kasar nan masu daraja.
“Ya dace a bayyana cewa a duk lokacin da aka gayyaci manyan mutane da kuma Baki na musamman don irin halartar irin wannan atisayen, ana ba su zabi don shiga atisayin harba Bindiga a matsayin wani sashi na bikin.
“Duk da haka, an wallafa faifan bidiyon na Honorabul Doguwa da nufin bata sunan sojojin Najeriya.” Inji shi.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamna: Al’ummar Oyo za sy zabi gwamna, Da ‘Yan majalisa 32
A yau Asabar al’ummar jihar Oyo za su zabi sabon gwamnan da zai yi wa jagoranci jihar na tsawon shekaru hudu.
Za a kuma zabi ‘yan majalisar dokokin jihar 32.