Rundunar Sojin Ƙasa ta tabbatar da hallaka Dakarun ta da dama a Niger
Rundunar Sojin Ƙasa ta tabbatar da hallaka Dakarun ta a Karamar Hukumar Shirori ta Jahar Niger, inda suka kashe Jami’an tsaro da dama
Ciki har da Sojoji da Ƴan Sanda.
Sun kuma sace ƴan kasar China da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abuja-Kaduna: Iyalan Sauran Matafiya 51 dake hannun Ƴan bindiga, sun yi gargaɗin karɓe wasu Ma’aikatun Gwamnati
Da yake tabbatar da harin, Rundunar Soji a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a nata ya fitar Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu yace a lokacin sun hallaka wasu ƴan Bindigar.
“Abun baƙin ciki, sojoji da dama sun hallaka a wurin musayar wuta a harin ta’addanci da aka kai masu.
” An gano wurin sannan an tura Dakarun Soji domin gano su, wanda tuni sun hallaka wasu ƴan Bindigar.
“Kwamanda na 1 na yankin tuni yaje wurin domin ɗaukar matakau”, inji sanarwar
A wani labarin kuma
Harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna: Iyalan Sauran Matafiya 51 dake hannun Ƴan bindiga, sun yi gargaɗin karɓe wasu Ma’aikatun Gwamnati
Iyalan sauran mutane 51 wadanda aka sace ƴan uwan su a harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna a ranar Juma’a sun yi gargaɗin ƙwace manyan Ma’aikatun Gwamnati a Kaduna da Abuja, sakamakon kasawar Gwamnati na ceto ƴan uwan su.
Ƴan bindiga sun yi gargaɗin kashe waɗanda ke hannun su, idan har Gwamnati bata biya su abubuwan da suka buƙata ba.
Kwanaki kaɗan da suka gabata, sun harbe mutum guda, suna tura wani saƙo ga Gwamnati cewa kashe su bazai yi masu wahala ba.
Biyo bayan wannan, iyalai da Abokanai na sauran waɗanda ƴan uwan su ke hannun ƴan bindiga, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun su Dr. Abdul’aziz Atta, ya bayyana tsoro na rasa iyalan su, musamman da rahoton nin da yazo na ci zon Macizai, da raunuka, wanda suke cigaba da shan wahala.
Atta, Wanda Mahaifiyar sa da Ƴar uwar sa sun a hannun su, ya bayyana damuwa akan yanda lafiyar su take a hannun su.
A cewar sa “kamar yadda take shine babu wani magani, babu wanda ya cire harsashi daga jikin su, kawai kayi tunanin yanda halin mutum zai kasance a Daji.
Yace duk da Gwamnati ta yi wani yunkuri, wanda 11 daga cikin ƴan uwan su aka sako su, amma dole sai ta ƙara sauri wajen ceto sauran mutanen da suka sace.