Rahotanni sun bayyana cewa, wasu yan bindiga sun farmaki kauyukan Buruku da Udawa dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda su ka kashe Manoma guda 8.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ne tabbatar da kai harin, sai dai bai yi karin haske ba dangane da yawan adadin mutanan da aka kashe a harin
Jagige ya kuma bayyana cewa, Yan bindigan sun farmaki kauyukan ne a ranar Juma’ar da ta gabata.
A cewar Mai magana da yawun dunrunar Yan sandan, ” Mun samu rahoton kai wani sabon hari a kauyuka biyu, Amma haryanzu bamu sami cikakken bayanai kan harin ba” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Malaman Tsangaya ta bukaci a dakatar da Fim din “A Duniya”
Kazalika Jalige ya ce “An Kai hari ga wasu Manoma dake kauyukan Buruku da Udawa, Amma haryanzu bamu samu cikakken bayanai kan harin ba, Amma da zaran Mun samu zasu sanar da al’uma” a cewar shi.
Amma wata majiya da Jaridar Dimokuradiyya ta samu ya bayyana mata cewa, Yan bindigan sun afka kauyukan ne da yawan gaske, inda suka fara harbi kan Mai uwa da wabi.
Kazalika ya ce, an kashe Manoma biyar ne a kan babba hanyar Buruku zuwa Birnin Gwari, ya yin da yan bindigan su ka kashe Mutum uku a kauyen Udawa.
Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta kawo musu dauki bisa yadda Yan bindiga su ka addabi yankunan biyu, da kai hare a kowa ce rana.