By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue dake yaki da ‘yan fashi da makami ta dakile yunkurin yin garkuwa da sabon mataimakin shugaban jami’ar Mkar UMM, Farfesa Zack Gundu a jihar Benue.
An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutanen.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa masu garkuwa da mutane an ce sun shirya yin garkuwa da Farfesa Gundu, amma daga baya sai suka canza shirinsu na farko inda suka tuntubi wanda suka yi niyyar yin garkuwa dashi wato mataimakin shugaban jami’ar (VC) ta wayar tarho, inda suka bukaci a basu zunzurutun kudi har naira miliyan goma domin ceto rayuwarsa.
Sai dai mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Gundu, ya yi kira da jajircewa tare da kai karar lamarin ga hukumar ‘yan sanda ta hanyar koke ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai.
Nan take ‘yan sandan suka kai dauki inda suka zakulo masu garkuwa da mutane zuwa wani gari mai suna Agbeede, dake karamar hukumar Konshisha ta jihar Binuwai, inda aka kama biyu daga cikin wadanda ake zargin.
Mataimakin shugaban jami’ar ta UMM, Farfesa Gundu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana yunkurin kashe shi a matsayin abin takaici.