By Abbas Yakubu Yaura
Ana ci gaba da aiki kan sabbin tsare-tsare wadanda za a gabatar da daftarin kwafin ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) don amincewa nan ba da jimawa ba, Ministan Kimiyya da fasaha da kere-kere, Dokta Ogbonnaya Onu, ya bayyana hakan.
Dr Onu ya bayyana haka ne a yayin bude taron majalisar zartarwa ta kasa kan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire a Abuja.
Ministan ya ce duk wasu tsare-tsare da ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayya ta bullo da su a baya sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasa.
A cewarsa, tsare-tsaren sun kuma taimaka wajen mayar da tattalin arzikin ya zama mai dogaro da ilimi da kirkire-kirkire sabanin yadda yake a baya inda tattalin arzikin ya kusan dogara da kayayyaki.
Dakta Onu ya jaddada bukatar daukacin jihohin su yi amfani da damar taron majalisar domin tsara hanyoyin ci gaban jihohinsu.
Tun da farko, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda mataimakinsa, Dakta Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce kowace kasa domin samun ci gaba mai dorewa dole ne ta runguma, turawa da kuma amfani da kimiyya, fasaha da kuma hanyar da ta dace da inganci.
Ya kara da cewa, tun bayan juyin juya halin kimiyya da fasaha da juyin juya halin masana’antu, an lura cewa duniya ta kasance mallakin wadanda suka san fasaha ba na masu sayen fasaha ba.
A halin da ake ciki, Dakta Onu ya ce taswirar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ta kasa,ta shekarar 2017-2030, dabarun kasa don gasa a cikin albarkatun kasa da bunkasa kayayyaki; Dokar Shugaban Kasa ta 5, Tsarin Man Fetur da Tsarin Fatu sun ba da gudummawa wajen inganta kimar gasar duniya a Najeriya kamar yadda kungiyar tattalin arzikin duniya (WEF) ta yi.