By Abbas Yakubu Yaura
Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, Muhammad Nasiha, ya yi murabus daga mukaminsa na majalisar dattawa a hukumance.
Hakan ya biyo bayan nadin da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi masa a matsayin mataimakinsa.
Nasiha ya maye gurbin Mahadi Ali, wanda majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige a makon jiya.
Idan dai ba a mantaba a ranar 23 ga watan Fabrairun ne dai Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar a zamanta da ta koma na ranar Laraba ta tsige Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar ba tare da bata lokaci ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Mustafa Jafaru Kaura ya fitar, ya ce an samu tsohon mataimakin gwamnan da dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
Bisa hakanne “Bayan samun adadin kuri’un da ake bukata kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, kakakin majalisar Magarya ya sanar da tsige Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar
Da yake karanta wasikar da aka aike wa majalisar dattawa a zauren majalisar, shugaban majalissar Sanata Ahmed Lawan, ya sanar da murabus din Nasiha ga majalisar.
An jiyo Nasiha ya yi murabus ya zama mataimakin gwamna a jiharsa ta Zamfara.