Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, a ranar Talata 8th Agusta, 2023 ya rantsar da sabon sakataren gwamnatin jihar (SGS) Barr Abdullahi Garba Faskari a gidan gwamnati, da ke Katsina.
Nadin Barr Abdullahi Garba Faskari a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ya zo ne bayan Arch Ahmad Musa Dangiwa ya yi murabus daga mukamin, bayan da ya samu mukamin minista a Gwamnatin Tarayya.
KARANTA NANKu Biya Haraji Don Ni Bazan Ciwo Bashi Don Yin Aiki Ba-Tinubu Ga Yan Najeriya
Malam Dikko Umaru Radda a lokacin bikin rantsuwar, ya ce nada Barr Abdullahi Garba Faskari ya biyo bayan samunsa da kwarewa da gogewa da aiki tukuru da dattakun da duk ake bukata ga aikin hidimta wa al’umma.
Mai Girma Gwamnan ya bukaci sabon Sakataren Gwamnatin jihar ta Katsina da ya yi amfani da irin basira da gogewa da yake da ita wajen ganin jihar ta ci gaba.
Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya ce Barista Abdullahi Garba Faskari ya aminta zai hidimta wa jihar Katsina a matsayin Sakataren Gwamnatin jiha, ba tare da ya yi la’akari da mukamin mataimakin Gwamna da ya taba rikewa ba, sai don ya hidimta wa jihar Katsina.
Bikin rantsuwar ya gudana ne a kan idon mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon. Faruq Lawal Jobe, Babban Jojin jiha Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, Grand Khadi na jiha da karin mambobin majalisar zartarwar jihar Katsina.
A WANI LABARIN KUMA
Tinubu Yayi Mana Alkawarin Cewar Zai Rage Yawan Motocin Da Yake Hawa-Kungiyar Kwadago
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Kwamaret Joe Ajearo ya bayyana cewar daga cikin tattaunawar da suka yi d shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan satin da ya gabata ya tabbatar masu da cewar zai yi kokarin rage yawan motocin da yake Nawa don rage kashe kudaden gwamnati sosai