Akalla mutane tara ne suka mutu sannan wasu sama da 80 ke kwance a asibiti sakamakon wata cuta da ta barke a gundumar Marsabit da ke arewacin Kenya. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Wani Jagora a yankin ya ce a cikin mutane tara da suka mutu, shida manya ne, uku kuma kananan yara ne dake tsakanin shekara daya zuwa uku.
KU KARANTA: Buhari Ya Yi Wani Sabon Nadi, Kwanaki 18 Kafin Sauka Daga Mulki
Kafofin yada labaran cikin gida sun ba da rahoton cewa, Yawancin mutanen da suka kamu da cutar sun nuna alamun mura, idanun su sun sauya zuwa launin rawaya, kumbura da kuma ciwon kai mai tsanani.
An gwada wasu daga cikin marasa lafiya inda aka gano suna dauke da cutar zazzabin cizon sauro amma likitocin sun ce wata cuta ce ta daban.
A wani labarin kuma, Bankwana Da Mulki: Gwamna Masari Ya Ziyarci Masarautun Katsina Da Daura
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya kai ziyarar ban kwana ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabair-Usman da na Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnan ya ziyarci Masarautar Katsina ne a ranar Larabar da ta gabata, kuma ya je Daura a ranar Alhamis a wani bangare na gudanar da ayyukan da ya kawo karshen wa’adinsa a ranar 29 ga watan Mayu.