Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Lahadi ya amince da sakin fursunoni goma sha daya daga gidan gyaran hali.
Wannan ya kasance bisa ga ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya bai wa gwamnan bisa shawarar majalisar ba da shawara kan hakin jinkai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Allah ne Kadai Ya San Shugabannin Najeriya Na Gaba – Dalibai Musulmi
El-Rufai, a wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Adekeye Muyiwa, ya bayyana cewa fursunonin da aka yi wa afuwa sun hada da wadanda ke zaman gidan yari na shekaru uku ko sama da haka.
Sannan da wadanda ke da watanni shida ko kasa da su kammala wa’adinsu, da kuma fursunonin da suka yi shekaru goma ko fiye da haka na hukuncin da aka yanke musu tare da nuna ɗabi’a masu kyau kuma waɗanda aka yanke musu hukunci suna fama da rashin lafiya mai yiwuwa su mutu.
Wadanda aka saki sune Yakubu Abdullahi, Habu Usman, Musa John, Abdullahi Abdulmumuni, Shamsu Usman, Mahadi Abdullahi, Abdullahi Lawal, Mohammed Anas, Kayode Gabriel Adenji, Sunday Iliya da Futune Mabuke.
Har ila yau, an gabatar da bayanai na sirri na jin kai ga gwamnan don tantancewa.
A yayin da yake gode wa jama’a bisa damar da suka samu na yi musu hidima, bisa fahimtarsu da goyon bayan da suka samu tsawon shekaru, gwamnan ya bukaci a ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da walwala, tare da fatan za a ci gaba da gudanar da aiki tukuru tun daga shekarar 2015 domin ganin jihar ta gyaru da inganta rayuwa na gwamnati mai zuwa.
A wani labarin kuma, 2023 Shekara Ce Ta Yanke Hukuncin Mai Tsauri – Gwamnan Kudu
Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya bayyana shekarar 2023 a matsayin shekarar yanke hukunci mai tsauri, yana mai cewa shekarar za ta iya kawo cikas ko kuma bata kasa, ya danganta da shawarar da ‘yan Najeriya za su dauka.
Emmanuel wanda ya yi magana a yayin bikin sabuwar shekara da aka gudanar a cocin United Evangelical, Aka road dake Uyo, ya jaddada cewa dole ne ‘yan Najeriya su dauki muhimman shawarwari da ake bukata domin ciyar da kasar gaba a shekarar 2023.