Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar da cewa; rigakafin cutar Korona zai samu, kuma za a samar da waann rigakafin miliyoyin al’umma, amma hakan zai samu ne a karshen shekarar 2021. Inda ta jaddada cewa a lokacin annobar na iya shafar mutum biliyan biyu.
A daidai lokacin da Kamfanoni da kasashe ke gasar samar da rigakafin Korona, sai ga Daraktan Kimiyya na WHO Soumya Swami-nathan tana bayyana cewa; yanzu haka akwai kimanin magungunan daban-daban har 200 a fadin duniya da ake gwaje-gwajensu a asibitoci, wanda tace, za a iya dacewa da daya ko biyu kafin karshen wannan shekara.
Babbar jami’ar WHO di ta bayyana rukunin mutane uku cikin al’umma da ta ce, za a fara bai wa maganin da zaran an same shi, da suka hada da jami’an kiwon lafiya da na ‘yan sanda da kuma gajiyayyu.