Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Sanata George Akume, ya bayyana kwarin guiwa game da makomar Najeriya, yana mai kira ga ‘yan kasar da kada su yi kasa a gwiwa a kan gwamnati.
Akume ya bayyana wannan kyakkyawan fata ne a wurin taron ‘National Solemn Assembly: Ranar Yabo, Ibada, da Godiya ga Allah ga Najeriya,’ da aka gudanar a Cibiyar Ecumenical ta kasa da ke Abuja karshen mako.
Karanta nanGobara Ta Tashi A Tashar Gidan Talabijin Na NTA Reshen Jahar Sokoto
Ya ce babu shakka Najeriya kasa ce mai hazaka, amma ya ce ta na bukatar jagora mai hangen nesa.
Don haka ya bukaci al’ummar kasar da su yi addu’o’in samun nasarar shugabancin kasar nan.
SGF ya yi kira da a ba da goyon baya da hadin kai ga shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke da nufin ciyar da kasar gaba ta hanyar samun nasara.
Ya ce muna buƙatar addu’a ba ga shugabanci kaɗai ba har ma da ƙasarmu. Muna da wani mutum mai ban mamaki, wanda ’yan Najeriya suka zaba ya jagoranci kasar nan na tsawon shekaru hudu. Yana bukatar addu’o’inmu don samun nasara.
Daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasar a lokacin kaddamar da shirin na Shugaba Tinubu, ya ce shi (Tinubu) ya yi hakan a Legas kuma zai yi wa sauran kasar nan.
A wani labarin kumaBa Zamu Kori Wike Daga PDP Ba-Shugaban Jam’iyar PDP
Akume, wanda ya sake nanata kwakkwaran imani kan yuwuwar Najeriya, yana mai ba da misali da albarkatun kasa da arzikinta, ya ce,babu shakka Najeriya kasa ce mai baiwa; muna da wadata a albarkatun kasa, da suka hada da ma’adanai.
Sai dai muna bukatar shugaba mai hangen nesa da zai yi mana jagora, kuma abin da Allah Ya azurta mu ke nan.
Ya kuma bukaci kafafen yada labaran Najeriya da su ci gaba da yada labaran abubuwan da suka hada kan kasa da kuma hada kan al’ummarta, maimakon mayar da hankali kan abin da ya raba su.