Babban bankin Kasa CBN ya jaddada kudirinsa na kare muradun miliyoyin ‘yan Najeriya marasa asusun banki da marasa aikin yi, wadanda galibinsu mazauna karkara ne.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Babban bankin ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na CBN, Mista Osita Nwanisobi, ya fitar, dangane da yadda ake shirin sake fasalin wasu kudaden Naira.
Nwanisobi ya bayyana jin dadinsa kan yadda masu hulda da bankunan suka mayar da martani ga shirin.
KARANTA KUMA Sake Fasalin Naira: EFCC Ta Tace Ta Sanyawa Wasu Gwamnoni Uku Idanu
Ya ce bankin na CBN ya jajirce wajen ganin an aiwatar da shi ba tare da wata matsala ba, ta yadda za a kiyaye mutuncin Naira ta hanyar rage yawan kudaden da ke wajen tsarin banki.
“CBN ya yi farin cikin ganin yadda al’umma suka mayar da martani ga wannan manufa ta hanyar kara yawan kudaden ajiya a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.
“CBN ya ci gaba da jajircewa wajen ganin an aiwatar da shirin ba tare da wata matsala ba domin tabbatar da cimma manufarta na kiyaye mutuncin takardar kudi ta cikin gida.
“Za a cimma hakan ne ta hanyar rage yawan kuɗaɗen da ke wajen tsarin banki da kuma yin amfani da su wajen aikata laifuka, tare da hana yin jabu da inganta hada-hadar kuɗi,” in ji shi.
Nwanisobi ya ce babban bankin na CBN yana daukar matakai na ganin ‘yan Najeriya marasa galihu ba su sha wahala ba saboda shirin sake fasalin Nairar. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Dole Ne A Dauki Matakin Hukunci Akan Matsalar Tsaro – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayar da shawarar a hukunta duk wanda aka samu da tabarbarewar tsaro kamar wanda ya yi sanadin harin da aka kai a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja ranar 5 ga watan Yuli.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya yi magana ne a yayin taron The People’s Townhall 2023, wani shiri kai tsaye da gidan talabijin na Channels ta shirya a Abuja a yammacin ranar Lahadi.