Sake fasalin Naira: Gaskiyar dalilin da yasa na amince da manufofin CBN – Buhari ya nemi afuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan batun sake fasalin kudin Naira.
A cewarsa, ba a bullo da shi don haifar da wahala ba, amma don bunkasa tattalin arziki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sakamakon zaben 2023: PDP na shirin kulla kawance da Peter Obi – Atiku
A watan Oktoban 2022, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana shirin sake fasalin kudin N200, N500, da N1,000.
Babban bankin ya kuma ce ranar 10 ga watan Fabrairu ne za a kayyade amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira wanda hakan ya haifar da karancin kudin.
A wani faifan bidiyo da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Uba Sani, ya saka a shafin Twitter a ranar Alhamis, Buhari ya ce: “Ina ba ku hakuri kan wahalhalun da canjin Naira ya haifar.
“An yi hakan ne domin bunkasa tattalin arzikin kasa, ba don a jawo wa kowa wahala ba.
A wani labarin kuma:Sakamakon zabe: Wike ne ƙashin bayan nasarar APC a Rivers – Okocha
Wasu ƴan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Ribas sun danganta nasarar jam’iyyar APC a jihar da kokarin gwamna Nyesom Wike.
Sai dai kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke biyayya ga Tony Okocha, tsohon shugaban ma’aikatan tsohon gwamna Rotimi Amaechi, sun dage cewa Wike na nan a jam’iyyar PDP.