Wakilinmu Sabi’u Musa
Wata kungiya a Jihar Sakkwato, ta ce Alhaji Atiku Abubakar, bashi da asali a jihar da kewayenta, ta kuma Gargadeshi da yaje ya nemi wani gun amma ba Sakkwato, ba.
Kamar yadda Mai Ritaya Aminu bala Sakkwato, ya Shedawa manema labarai, cewa tsohon mataimakin shugaban kasa da ya daina Alakanta kanshi da Sakkwatawa, domin a wurno bashi da na saba ta kusa ko ta nesa da wani a cikin gari ko gefe.
Aminu, ya cigaba da bayyana cewa a yanzu ne zai bayyana hakan ya manta abinda ya fada a shekarar 2003 duk Wanda yake Kano, Jigawa, da sauran Yankunan Arewa maso yamma ba zai manta irin kalaman da Atiku, ya ringa yi a baya ba.
Bala, ya kara da cewa tun wuri ka nemi asalinka amma ba wurno ba. kuma ba mu yarda da duk ikirarin ka ba, inji shi.