- Gwamnan Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu, ya amince da a biya albashin watan Yuni ga kafatanin ma’aikatan jihar da kuma ‘yan fansho
- Hakan dai na daga cikin alkawuran da ya dauka a ya yin yakin neman zabe na tabbatar da biyan albashi cikin gaggawa
- Gwamnan ya yi kira ga ma’aikatan jihar da su mayar da martanin da ba a saba gani ba wajen kiyaye lokacin zuwa aiki
Gwamnan Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu, ya amince da a biya albashin watan Yuni ga ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi, malamai da kuma ‘yan fansho a fadin jihar, Tribune Online ta rawaito
Hakan dai na daga cikin alkawuran da ya dauka a ya yin yakin neman zabe na tabbatar da biyan albashi cikin gaggawa.
KARANTA WANNAN: DSS Ta Bankado Wata Kulla-Kullar Shirya Kai Hari a Wuraren Ibada Da Na Shakatawa
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun sakataren yada labarai na gwamnan Malam Abubakar Bawa.
“Wannan karimcin na da nufin ganin ma’aikatan gwamnati a fadin jihar su gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa cikin sauki.
Gwamnan ya kara tabbatarwa ma’aikata a jiharsa da gwamnatin sa bisa jajircewar sa na farfado da martabar ma’aikatan da suka rasa ta hanyar tabbatar da jin dadin ma’aikata a kowane lokaci.
Don haka Gwamnan ya yi kira ga ma’aikatan jihar da su mayar da martanin da ba a saba gani ba ta hanyar kiyaye lokaci, gaskiya da sadaukar da kai ga aikinsu.
Aliyu ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa gwamnati mai ci addu’a domin samun nasara wajen biyan bukatunsu.
A wani labarin kuma, PDP Ta Koka Kan Tsoma Bakin Sarakunan Gargajiya A Rikicin Majalisar Dokokin Nasarawa
Jam’iyyar PDP reshen jihar Nasarawa ta koka da yadda sarakunan gargajiya suke tsoma baki a harkokin siyasa
PDP tace hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar a ranar 6 ga watan Yuni, 2023
PDP tayi zargin cewa da yawa daga cikin sarakunan gargajiya suna yi wa talakawansu barazana wadanda zababbun mambobin jam’iyyar ne