Gwamnatin tarayya ta ce marasa galihu 32, 236 ne a Kaduna za su amfana da tallafin naira dubu biyar duk wata a karkashin shirinta na tallafa wa marasa galihun da aka kira ‘Conditional Cash Transfer (CCT)’.
Shugaban sashen CCT a Kaduna, Hajiya Hauwa Abdulrazaq ce ta bayyana hakan a yayin zantawarta da kamfanin dillacin labaran Nijeriya a Kaduna a ranar Talata.
CCT shiri ne na taimakon gidaje masu kananan karfi a fadin kasar, domin tallafawa walwalarsu.