Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim Bamba ya rasu
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Dr. Ahmad Ibrahim Bamba wanda aka fi sani da Dr Ahmad BUK ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya.
Dan sa Ahmad Muhammad Ahmad ya sanar da rasuwar mahaifinsa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a ranar Juma’a.
Ya ce za a yi jana’izar marigayin a masallacin Darul Hadith, Tudun Yola, cikin birnin Kano da misalin karfe 1:30 na rana.
Marigayi Dr. Ahmad ya kasance malami a Sashen Larabci da ke BUK kafin ya yi murabus ya shiga aikin wa’azin Musulunci gaba daya.