Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa kuma Sanata mai wakiltar mazabar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe zai sauka a ranar Laraba a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa.
Abaribe, wanda ya karbi shugabancin marasa rinjaye a 2019, an zabe shi ne a inuwar jam’iyyar PDP amma ya koma jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) sakamakon rikicin da ya ce ya ki ci ya ki cinyewa a lokacin da yake neman tikitin takarar gwamna jihar sa domin shiga zaben 2023.
Ko da yake ya kasance a ranar Talata don gudanar da ayyukan majalisa bayan hutun sama da wata guda inda ‘yan majalisar suka dauki lokaci don zaben fidda gwani da jam’iyun siyasa suka yi, amma bai sanar da ficewarsa daga PDP a hukumance ba.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa tun daga lokacin ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Ibrahim Lawan, amma an dage wasiƙar don karantawa a ranar Laraba, inda Abaribe zai yi murabus daga bisani kuma za a kai shi sabuwar kujerarsa
Lawan, ya kuma kara tabbatar da cewa jagoran ‘yan adawa ya sauya sheka, yana mai cewa za a sanar da cikakken bayanin ranar Laraba.
Kafin Lawan ya yi magana kan Abaribe, Sanata Gabriel Suswam mai wakiltar mazabar Benue ta Arewa maso Gabas ya tabo batun wajan jawo hankalin majalisar kan matsayin Abaribe.
Sauran mambobin da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi, da Adamu Aliero.