Sanata Uba Sani Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Ga Ɗaliban Da Ke Koyon Sana’o’i
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya bada tallafin tsabar kudi na Naira Miliyan 20 ga cibiyar horas da matasa sana’o’i ta Bayero.
Ɗaliban sama da Dubu 2000 ne ke amfana da shirin horas da Sana’oin da aka zaɓo daga Mazaɓu 12 na Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zabe: IGP Ya Ba Da Umarnin Hana Zirga-Zirgar A Baben Hawa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Uba Sani ya fitar a shafin sa na Facebook, da Jaridar Dimukuradiyya ta samu.
A cewar sa, ya bada tallafin ne domin taimakawa waɗanda zasu amfana da shirin koyar da Sana’oin, don su samu ilmi da zai sanya su zamanto masu dogaro da Kawunan su.
Ya rubuta sanarwar kamar haka “An karrama ni da zama baƙo na musamman a wajen bikin yaye dalibai na cibiyar horas da Sana’oi ta Bayero Skills Acquisition/Training Programme tare da sama da mutane 2000 da aka zabo daga gundumomi goma sha biyu (12) na karamar hukumar Kaduna ta Arewa. Na ba da gudummawar Naira miliyan 20 don taimaka wa su dogara da kansu.