Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani a karkashin jam’iyar APC a cigaba da kokarin Gwamnatin jihar ya bayar da tallafin Naira Miliyan 20,000,000 ga ‘yan kasuwa marasa karfi, Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook inda ya bayyana hakan don taimaka musu wajen samun damar ’yancin mallakar shaguna a kasuwannin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Wasu Iyaye Suka Taimakawa ‘Yarsu Yi Jana’izar Kifinta Da Kuma Zaman Makoki Bidiyon Ya Dau Hankali
Sannan ya kuma kaddamar da wasu katafarun kantuna guda biyu da gwamnatin jihar Kaduna ta gina ta hanyar hadin gwiwar masu zaman kansu domin tallafa wa ‘yan kasuwa marasa karfin Jari wajen mallakar shagunansu.
Sanata Uba sani ya saba tallafawa Yan kasuwa tun bayan da ya zama Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya.
Kazalika kawo Yanzu shine Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Mafi samun karbuwa da chancanta kamar yadda wasu al’kaluma suka bayyana.
A wani labarin kuma, Yadda Pretty Mike Ya Jagoranci ‘Yan Mata 16 Masu Rufaffen Ido Zuwa Bikin Aure Ya Dauki Hankula
Shahararren dan Najeriyar Pretty Mike a salon da ya saba yi ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta ina ya halarci wani bikin aure.
Domin magance halin da kasar ke ciki, Mike sanye da kayan sarki mai ido daya wanda ya jagoranci wasu mata masu rufaffen Ido zuwa wajen liyafar auren.