A yau Asabar Sanata Uba Sani ya taya al’ummar Musulmi murnar shigowar watan Ramadan, kamar yadda ya bukace su da su ci gaba da hada kan su tare da yin koyi da darasin watan na Ramadan.
Sanata Uba wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattijan kasar nan, ya ce wannan lokacin yana da matukar muhimmanci yayin da ‘yan Najeriya ke neman mafita da kuma ja-gorancin Allah daga kalubalen da suke fuskanta.
Ya ce watan Ramadan, wanda lokaci ne na tunani na ruhi, kamewa, sadaukarwa da addu’a ga Allah madaukaki, Kuma daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.
A cewarsa, Ramadan lokaci ne na yin amfani da kyawawan dabi’u yadda ya kamata; hakuri da kai, afuwa, sadaukarwa, soyayya da kuma lokacin taba rayuwar marasa galihu da masu rauni a cikin al’umma ta hanyar ayyukan agaji.
Ya bukaci kowa da kowa ya yi amfani da wannan damar na watan Ramadan don yin tunani a kan matsalolin da ke addabar Nijeriya, kuma a yi addu’a sosai domin Allah ya kawo mana dauki.