Sanata Uba Sani Ya Halarci Taron Walimar Cin Zaɓen Tinubu Da Musulmai Suka Shirya
Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya samu gayyata ta musamman daga gamayyar Kungiyar Addinin Islama a wani taron walima da suka shirya domin samun nasarar Bola Ahmad na jam’iyar Apc.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Bukaci Bangarorin Siyasar Kasar Chadi Su Marawa Dimokradiyyar Mika Mulki Baya
Sanata Uba Sani yace “A yau, na halarci taro na musamman wanda Kungiyar Muslim League for Accountability (MULAC) ta shirya domin murnar samun nasarar babbar jam’iyyarmu ta APC da dan takararta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa na ranar Asabar daya gabata.
Sanata Bola Ahmad Tinubu Tsohon gwamnan jihar Lagos ya samu nasara a zaben daya gabata na ranar Asabar.
Sanata Uba Sani ya yi kira ga Gamayyar musulman da su fito ranar Asabar mai zuwa tare da zaɓen sa domin cigaban Jihar Kaduna.