Sanata Uba Sani Ya Taya Tinubu Murnar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa
Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyar Apc Sanata Uba Sani ya taya Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa.
A Sakon sa na taya murna ga Shugaban Kasar Nageriya Mai jiran Gado Sanata Bola Tinubu yace “Ina mika sakon taya murna na ga mai dauke da tutar jam’iyyar mu, Jagaban mai girma Sanata Bola Ahmed Tinubu bisa gagarumar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa da aka kammala.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gawuna Ya Taya Tinubu, Shettima Murnar Zama Shugaban Kasa Da Mataimaki
“Ina yabawa mambobin jam’iyyar APC da magoya bayan jam’iyyar APC bisa namijin kokarin da suka yi wajen ganin an cimma wannan gagarumin nasara da ba za a manta da su ba”. Inji shi.
Ya kara dace wa “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kai mai nasara ne kuma mai Samar da ci gaba kuma mai karfafa wa mutane ne”.
“Kai mai gina Al’umma ne. Mutum ne mai alkhairi. Ina da tabbacin za ka maimaita irin gagarumin ci gaban da ka samar a jihar Legas Zuwa ga fadin kasar nan. Tare da goyon bayanmu na hadin gwiwa zai kai kasarmu a matsayi mafi girma.
Ya ce “Wannan shine lokacin da dukkanmu za mu rufe matsayi. Zaɓaɓɓen Shugabanmu zaka gudanar da gwamnati mai cike da manufa. Zai sa ‘yan Nijeriya da Nijeriya su yi alfahari. Lalle wannan shi ne alfijir na wani zamani mai daraja”.
Sanata Uba sani na kallon hasken samun Nasara a zaben gwamna Mai zuwa.