A cigaba da zagayen da Ɗan takarar Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba sani keyi ga masu ruwa da tsaki a faɗin Jahar, a Jiya Talata ya kai ziyara a majalisar Dokokin Jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa, Sanatan ya bayyana Cewa jindaɗin sa na yadda ziyarar daya ke kaiwa, ke cigaba da taka muhimmiyar rawa a Takarar Gwamnan Jahar Kaduna daya keyi.
Tawagar sa ta haɗa da tsoffin Shugabannin majalisar jihar kaduna Rt. Hon. Bashir Zubairu Birningwari da Rt. Hon Aminu Shagali, inda ya samu kyakkyawar tarba daga ƴan majalisar Dokokin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Yan bindiga Sun Harbe Ango Mai jiran Gado, Mako Daya Kafin A Sha Biki
A cikin jawaban daya gabatar a Majalisar ya bayyana matsayin Majalisar a tsarin Dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa ita ce ta jama’a da kuma katangar da za ta bi wajen kawar da wuce gona da iri.
Uba Sani ya cigaba dacewa, ta hanyar ayyukan sa ido na Majalisar, zata tabbatar da cewa an aiwatar da manufofi da ayyuka cikin gaskiya da riƙon amana, a saboda haka, “cibiya ce data kasance mai muhimmanci da dole ne a mutuntata da kuma ɗorewarta idan ana son ƙarfafawa da zurfafa dimokuraɗiyyar mu”.
“Saboda muhimmiyar rawar da majalisa ke takawa, dole ne in tuntuɓi mambobinta don sanar da su burina na tsayawa takarar Gwamna tare da bayyana musu irin yadda za mu kai jihar Kaduna mataki na Gaba baki daya”. Inji Uba Sani.
Uba Sani ya Ƙara dacewa “Na tabbatar wa ƴan uwa cewa, idan na samu wannan aikin na jama’a, zan kulla ƙawance mai ƙarfi da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, don ba da damar zartar da manyan ayyuka, da suka shafi jama’a”.
Ɗan Takarar Gwamnan ya bayyana cewa takarar shi ta gwamna ta zo ne a bisa burin da yake da shi na karfafawa tare da gina kyawawan abubuwan ci gaban Gwamna Mal. Nasiru Ahmad El-Rufai.
Ya bayyana irin namijin ƙoƙarin Majalisar, yana mai cewa Majalisar ta na da hannu a cikin nasarorin da Gwamnatin El-Rufai ta samu.
Sanata Uba Sani yace Dangantaka tsakanin ɓangaren Zartaswa da na Majalisa a jihar Kaduna, abin koyi ne a ɓangaren haɗin kai da hadin gwiwa.
“Ina fata Majalisa mai zuwa za ta yi amfani da gogewar Majalisar da ke yanzu kuma ta yi aiki tare da ni idan Allah ya aminta aka ba ni damar na zama Gwamna” Inji shi.
Ya bayyana godiyar sa ga kakakin Majalisa da ƴan majalisar Dokokin Jihar Kaduna da irin kyakkyawar tarbar da suka yi mashi.
Jim Kaɗan, bayan ganawar sa da Majalisar, a jiya dai Sanatan ya Ƙara ganawa da Kansiloli tare da Sakatarorin Ƙananan Hukumomin a duk kokarin sa na zama Gwamnan jihar ta kaduna.
Comments 1