Sanata Uba Sani yakai ziyara ga Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nemi Tabarraki
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna kuma Sanatan Kaduna ta Tsakiya yakai ziyara ga Shehin Malamin Musulunci Sheikh Ɗahiru Bauchi domin neman Tabarraki a ƙoƙarin shi na tsayawa Takarar Gwamnan jihar Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yanke wa tsohon shugaban kasar Burkina Faso hukuncin daurin rai da rai kan kisan Sankara
Daya yake jawabi Jim kadan bayan ziyarar, Sanatan yace “Na Kai ziyarar Girmamawa ne ga Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a gidansa dake Kaduna.
“Sheikh Ɗahiru Bauchi ya kasance fitaccen malamin Addinin Musulunci ne kuma hazikin malami da ya tsaya tsayin daka a fagen ilimi. Hakika iliminsa ya kasance mai tasiri a cikin al’ummarmu a yau” Inji Sanata Uba Sani.
A cewar Uba Sani “Ya yi mani addu’a sannan kuma ya yi amfani da damar yin addu’a ga jaha, da ƙasar mu baki ɗaya dangane da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan.
Sanata Uba sani na daya daga cikin ƴan takarar dake Neman zama Gwamnan jihar kaduna a Babban zaƁen 2023 Mai zuwa.