By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin gudanarwa na wani sabon masallacin Juma’a da ke bayan babban bankin Najeriya (CBN) da ke Abuja, ya nada tsohon babban limamin masallacin Juma’a na shiyyar E, Apo Legislative da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid.
DUBA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Gano Wasu ‘Yan Uwa Uku Makonni Biyu Da Bacewar A Abuja
Sheikh Nuru Khalid zai ja-goranci sallar juma’a daga ranar 8 ga watan Afrilu a sabon masallacin.
Kwamitin kula da masallacin ya kori sheikh Khalid ne sa’o’i da suka gabata saboda sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a daren ranar Litinin ta makon daya gabata.
A lokacin da yake wa’azin, ya yi wa gwamnati kaca-kaca a kan gazawarta na shawo kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashe a kasar.
Sai dai ya bayyana dakatar da nadin nasa da kwamitin gudanarwa na masallacin ya yi a matsayin wani farashi da ya wajaba ya biya domin tantance talakawan da ke cikin wahala da fadin gaskiya ga mulki.
Khalid ya ce: “Da yardar Allah Ta’ala zan jagoranci sallar juma’a a wannan sabon masallacin, domin a matsayinmu na malamai muna bukatar wani dandali don gudanar da ayyukanmu.
“Akwai wani masallacin Juma’a da muka gina a bayan CBN Quarters, a Abuja; Yanzu zan jagoranci sallar juma’a a wurin.”