Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf ya rasu
Sheikh ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekaru 86, kamar yadda fadar masarautar ta bayyana.
Mutuwar tasa na zuwa ne bayan shafe shekaru uku yana mulki inda aka sha fama da rigingimun siyasa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hukuncin Kotun Koli na shirin hana Nnamdi Kanu adalci ne – IPOB
“Cikin bakin ciki muna jimamin rasuwar Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah, Sarkin Kuwait,” in ji wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin na kasar.
Tashar ta yanke shirye-shiryenta na yau da kullun kuma ta canza zuwa watsa shirye-shiryen karatun kur’ani kafin sanarwar.
A watan Nuwamba, an kwantar da Sheikh Nawaf a asibiti “saboda matsalar lafiya ta gaggawa”, a cewar kamfanin dillancin labarai na KUNA. Ba ta bayar da cikakken bayani game da rashin lafiyarsa ba, amma daga baya aka bayyana cewa yana cikin kwanciyar hankali.
Bisa la’akari da shekarunsa, damuwa game da lafiyarsa ya zama ruwan dare a lokacin mulkinsa.
Sheikh Nawaf ya hau kan mukamin yarima mai jiran gado a shekara ta 2006, wanda dan uwansa Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya nada. Ya rike mukamin sarki bayan rasuwar Sheikh Sabah a watan Satumbar 2020 yana da shekaru 91.
A shekarar 2020, Sheikh Nawaf ya fuskanci kalubalen tafiyar da harkokin tattalin arziki ta hanyar rikicin da ya janyo faduwar farashin mai.
Yarima mai jiran gado na yanzu, Sheikh Mishal al-Ahmad al-Sabah, wani dan uwa uba, yana da shekaru 83 a duniya.
Yanzu an mai da hankali kan ko iyali za su nada wani matashi mai mulki
A wani labarin kuma:Rikicin Rivers: Ba na fada da Wike – Gwamna Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Riba ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ba wai yakar kowa ba.
Fubara ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da rukunin gidaje 20,000 na masu karamin karfi a jihar a Mbodo-Aluu, daura da titin filin jirgin sama na kasa da kasa a karamar hukumar Ikwerre a ranar Juma’a